rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sabon harajin da Amurka ta kakabawa kayan China ya fara aiki

media
Chine_politique 网络。

A yau jumaá ne Karin 25% na harajin dala biliyan 50 da Amruka ta saka kan hajojin da ke zuwa kasar daga kasar China zai fara aiki.

Amruka dai na zargi China ne, da haifar mata da gibi mai yawa kan harakokin kasuwanci, tare da sace fasahar kamfanoninta dake cibiyoyinsu a kasar ta china.


Tun lokacin da Amruka ta bayyana aniyar ta na yiwa hajojin dake fitowa daga china zuwa kasarta Karin harajin 25%, Mahukumtan Pekin su ka bayyana aniyar mayar da martini ma zafi, wanda za a iya cewa idan ya wakana wata kila shine farkon barkewar yakin tantagarya na kasuwanci tsakanin manyan kasashen mafiya karfin tattalin arriziki a duniya.

Ana jajibirin soma aiki da sabon karin harajin na Amruka kan China cikkunan kasuwanin hannayen jari na duniya suka duri ruwa, kan illar da rikicin kasuwanci da ke tsakanin kasashen 2 zai iya haifarwa tattalin arizikin duniya.

karin 25% , a cikin harajin dala bilina 50 ga kasar ta china, zai fara ne da zub dala biliyan 35 a tashin farko, sai kuma dala biliyan 16 su biyo baya, tare da sharadin cewa, idan kasar Chinar ta mayar da marani d kan hajar da kasar Amruka ke shigarwa a kasarta, Amrukar za ta sake lissafa wasu hajojin kasar ta China ta saka a cikin sabon harajin.

Da farko dai chinar na biyan harajin biliyan 25 ne na hajarta da take shigarwa a kasar Amruka a yayin da amruka ke biyan biliyan 26 kan tata hajar dake shiga kasar China

kwarara kan tattalin ariziki Cécilia Bellora, ta cibiyar binciken tattalin ariziki ta duniya (CEPII) ta ce, fanonin kasuwancin kasashen 2 da rikicin ya shafa sun bambanta. A bangaren China harajin, ya shafi injina samar da kere keren zamani da ake amfani da su a masanaántun samar da kayayaki, a yayin da a bangaren Amruka harajin na china, ya shafi Motoci, man girki, da kuma waken soya.