Isa ga babban shafi
Thailand

An yi nasarar ceto yara 8 da suka makale a kogo

Jami’an agaji sun yi nasarar ceto karin yara 4 daga cikin dalibai 12 da malaminsu daya da suka shafe sama da makwanni biyu makale cikin wani kogo arewacin kasar Thailand.

Jami'an agaji da na tsaro yayin sauko da daliban da aka ceto daga kogo daga cikin jirgi mai saukar ungulu na soji zuwa motar asibiti, a filin jiragen sama na birnin Chiang Rai, da ke Thailand, 9 ga watan Yuli, 2018.
Jami'an agaji da na tsaro yayin sauko da daliban da aka ceto daga kogo daga cikin jirgi mai saukar ungulu na soji zuwa motar asibiti, a filin jiragen sama na birnin Chiang Rai, da ke Thailand, 9 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Athit Perawongmetha
Talla

Bayan shiga rana ta biyu a aikin ceton, jami’an agaji sun yi nasarar ceto jimillar dalibai 8 kenan, yayin da rage saura guda hudu da kuma malaminsu.

A ranar 23 ga watan jiya ne, yaran da shekarunsu ke tsakanin 11 zuwa 16 da kuma kocinsu mai shekaru 25, suka shiga cikin kogon Tham Luang a dai dai lokacin da ake tafka ruwa kamar da bakin-kwarya bayan sun kammala atisayen kwallon kafa.

A ranar 24 ga watan na jiya ne, jami’an tsaro suka gano sahun kafa da na hannu na wadannan yara a hanyar kogon, lamarin da ya sa aka fara gudanar da aikin neman su.

A ranar 25 ga watan Yuni ne, wasu sojin ruwa kuma gwanayen ninkaya suka kutsa cikin kogon, yayin da aka kafa wata rumfar wucen-gadi don gudanar da addu'o'in ceto yaran.

A ranar 26 ne kuma, gwanayen ninkayar suka isa wata mahadar hanya mai tazarar kilomita mai yawa zuwa cikin tsakiyar kogon, amma sun gaza karasawa ciki saboda ambaliyar ruwa wadda ta toshe mashigin wurin da yaran suka fake.

A kashe-garin ranar ne, wata tawaga da ta kunshi kwararru daga Amurka da Birtaniya ta iso Thailand don ceto yaran.

Bayan shafe wasu ‘yan kwanaki , gwanayen ninkaya suka yi nasarar gano yaran 12 da kocin nasu a raye, yayin da a ranar 3 ga wannan wata aka isar da abinci da magunguna ga yaran duk da cewa, za su ci gaba da zama a cikin kogon kafin kammala dabarun futo da su.

Sai dai a ranar Lahadi ne aka fara ceto yaran daya bayan daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.