Isa ga babban shafi
Turkiya

Erdogan na ya karbi rantsuwar wa'adi na biyu

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi rantsuwar ci gaba da jagorantar kasar wa’adi na biyu, a karkashin wani sauyi na kundin tsarin mulkin da ya ba shi karin karfin fada-a-ji da kuma aiwatar da sauye-sauye kai tsaye.

Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan Kayhan Ozer/Presidential Palace
Talla

Bikin na yau na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban ya kori ma’aikata dubu 180 saboda zargin su da hannu a wani yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Erdogan zai sha rantsuwar ne a zauren Majalisar Dokokin Kasar kafin daga bisani a rakashe a fadarsa tare da wasu tsirarun shugabannin kasashen duniya da suka halarci bikin.

‘Yan adawa na sukar salon mulkin Erdogan da suke kallo a matsayin kama-karya musamman ma a baya-bayan da aka samar da dokar da ta kara ma sa karfin ikon da wani shugaba a Turkiya bai samu a tsawon shekarun da suka shude.

Kusan shekaru biyu kenan da gwamnatin Erdoga ta yi nasarar dakile wani yunkurin juyin mulki a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.