rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Japan Canjin Yanayi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 100 sun mutu a ambaliyar ruwa a Japan

media
Kimanin mutane miliyan 2 suka rasa muhallansu saboda ambaliyar ruwa a Japan Kyodo/via REUTERS

Firaministan Japan, Shinzo Abe ya soke ziyarar da ya shirya kaiwa kasashen ketare hudu bayan ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 100 a kasar.


Mr. Abe ya shirya kai ziyarar aiki a kasashen Faransa da Belgium da Saudiya da kuma Masar daga ranar Laraba, amma ya soke saboda wannan ibtila’in da ya afka wa kasarsa kamar yadda ofishinsa ya sanar.

Jami’an agaji sun bayyana fargabar karuwar asarar rayuka, duba da yadda wasu kafofin yada labaran kasar suka rawaio cewa, har yanzu akwai tarin mutanen da suka bace.

Firaminista Abe, ya nuna damuwa kan jinkirin da ake samu wajen aikin ceto wadanda ibtila’in ya ritsa da su.

Sama da mutane miliyan biyu ne ambaliyar ruwan ta tilasta wa tserewa daga muhallansu, bayan manyan kogunan da suka tumbatsa suka shafi yankunan yammaci da tsakiyar kasar.

Hukumar Lura da Yanayi ta Japan ta yi gargadin cewa, akwai sauran hadari a gaba, ko da kuwa an samu sassaucin ruwan sama, domin kuwa yankunan da ambaliyar ta shafa na fuskantar barazanar zabtarewar kasa.