rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sakataren ficewar Birtaniya daga EU ya yi murabus

media
Sakataren Ficewar Birtaniya daga Turai mai murabus, David Davis REUTERS/Hannah McKay

Sakataren da ke jagorantar tattaunawar ficewar Birtaniya daga Kungiyar Kasashen Turai, David Davis ya sauka daga mukaminsa, a dai dai lokacin da Firaminista Theresa May ke kokarin hada kan 'yan jam’iyyarta kan shirin kulla dangantakar tattalin arziki mai karfi da Kungiyar Turai bayan ficewar.


Mr. Davis ya ce, daga yanzu, ba shi ba ne mutumin da ya dace ya jagoranci shirin gwamnatin Birtaniya na ficewa daga Tarayyar Turai.

Murabus din Davis na matsayin wani gagarumin koma-baya ga gwamnatin May wadda ke kokarin shawo kan wasu ministoci don ganin sun amince da muradun da take fatan cimma bayan ficewar.

Kafofin yada labaran Birtaniya sun ce, bayan saukar David Davis, wasu ministoci biyu, Steve Baker da Suella Braverman su ma sun yi murabus.