rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Thailand Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugabannin duniya na ci gaba da taya murnar ceto 'yan kwallon Thailand

media
Ita ma kungiyar Manchester United ta gayyaci yaran da wadanda suka taimaka wajen ceto su domin su ziyarce ta a kaka mai zuwa. ©REUTERS/Athit Perawongmetha

Shugabannin Kasashen duniya da taurarun Yan kwallo sun bi sahun kasashen duniya wajen bayyana farin cikin su da nasarar da aka samu na ceto yan kwallon Thailand da mai horar da su da suka makale a cikin kogo.


Shugaban Amurka Donald Trump na daga cikin na farko da suka taya sojin ruwan kasar murna saboda yadda suka jagoranci aikin, yayin da Theresa May, Firaministan Birtaniya ta yaba daukacin wadanda suka bada gudumawa wajen ceto yaran.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantinno ya gayyaci yaran zuwa Rasha domin kallon was an karshe na cin kofin duniya, sai dai likitoci sun ce yaran ba za su iya tafiyar ba.

Ita ma kungiyar Manchester United ta gayyaci yaran da wadanda suka taimaka wajen ceto su domin su ziyarce ta a kaka mai zuwa.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da yan wasan ta Toni Kroos da Mezut Ozil, da ministan harkokin wajen Belgium duk sun bayyana farin cikin su da ceto yaran.