Isa ga babban shafi
Ebola-Spain

Ana bincike kan maganin Ebola a Spain

Kwararrun Kiwon lafiya na Spain na gudanar da bincike kan wani nau’in maganin riga-kafin kamuwa da kwayoyin cutar Ebola da ake kallo a matsayin irinsa na farko a duniya

Cutar Ebola ta kashe kimanin mutane dubu 11 da 300 a kasashen Afrika uku
Cutar Ebola ta kashe kimanin mutane dubu 11 da 300 a kasashen Afrika uku KENZO TRIBOUILLARD / AFP
Talla

Hukumomin Kiwon lafiya na birnin Madrid da ke Spain sun ce, tuni aka fara amfani da maganin wanda rukunin kamfanonin sarrafa magunguna na Merck ya samar.

Sai dai kawo yanzu maganin na yakar wata kwayar hallita daya ce kadai da aka yi wa lakabi da “Zaire” a maimakon yakar kwayoyin halitta biyar da ke sabbaba kamuwa da cutar Ebola.

Duk da cewa ba a bai wa kamfanin izinin tallata maganin a kasuwa ba, amma Majalisar Dinkin Duniya ta amince a yi amfani da shi akan mutanen da suka kamu da Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo a cikin watan Mayun da ya gabata da zimmar gaggauta shawo kan cutar wadda ta kashe kimanin mutane dubu 11 da 300 a kasashe uku na yammacin Afrika a tsakanin shekarar 2013-2015. abin da ya tayar da hankulan kasashen duniya.

Kwararrun sun kwashe tsawon watanni suna bincike a wasu asibitoci da ke Spain, in da suke nazartar samfurin jinin da aka dauka daga mutanen da suka warke daga wannan cuta ta Ebola.

Daya daga cikin masu binciken, Rafael Delgado ya shaida wa manema labarai cewa, babban kalubalen da suke fuskanta, shi ne yadda kwayar cutar ke kare kanta daga duk wani magani, amma wani lokaci, ta kan bude kafar samun galaba akanta na dan kankanin lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.