rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ireland Isra'ila Falasdinawa Palestine Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ireland ta haramta kayayyakin Isra'ila saboda Falasdinawa

media
Gwamnatin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ta bayyana bacin ranta kan matakin Ireland Abir Sultan/Pool via Reuters

Majalisar Dokokin Kasar Ireland ta amince da dokar haramta sayen kayayakin da Isra'ila ta sarrafa a kamfanonin da ta gina cikin filayen Falasdinawa kamar yadda dokokin Majalisar Dinkin Duniya suka tanada.


'Yan Majalisu 25 suka amince da kudirin, yayin da 20 suka hau kujerar naki.

Gwamnatin kasar ta ce, aiwatar da dokar za ta ci karo da manufofin Kungiyar Kasashen Turai kuma hakan na iya taimakawa wajen haifar da matsalar cinikayya tsakanin Ireland da kasashen da ke yankin.

Sanatan da ya gabatar da kudirin, Francis Black ya ce, ya san cewa aiwatar da dokar za ta yi wuya amma dai sun bayyana matsayinsu.

Kasar Isra'ila cikin fushi ta bayyana matakin a matsayin mai tattatre da hadari, yayin da Kungiyar Falasdinu ta yi na’am da shi.