An soma taro na NATO a Turai
Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci kasashen dake cikin kungiyar kawancen tsaron NATO da su biya Amurka kudaden da take zubawa wajen gudanar da ayyukan kungiyar, yayin da ya sauka a Brussels domin halartar taron kasashen.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A cikin jirgin sama dake dauke da shi ne dai Donald Trump ya aike da sakon cewa kasashen kungiyar NATO da yawa da ake bukatar su kare, ba su nuna damuwa ba sosai wajen sauke bukatar kashi 2% wanda yayi karanci ma ainun.
Amma kuma tsawon shekaru basa iya biyan kudaden da ake bukata daga garesu na tafiyar da kungiyar.
Yana mai kawo ayar tambaya cewa suna iya biyan Amurka kuwa kudaden da take kashewa.
Yana mai cewa Kungiyar NATO bata yiwa Amurka adalci ba a yarjejeniyar da aka shata da Amurka.
Shugaban kungiyar kasashen Turai Donald Tusk ya gargadi Trump da ya mutunta kasashen dake kawance da kasar sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu