rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Jamus Rasha Tarayyar Turai NATO/ OTAN

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump da Merkel sun yi musayar kalamai a NATO

media
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Jonathan Ernst/File Photo

Shugaban Amurka Donald Trump da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel sun yi musayar zafafan kalamai a yayin taron Kungiyar Tsaro ta NATO da ke gudana a birnin Brussels a wannan Laraba.


Wannan na zuwa ne bayan shugaba Trump ya bayyana Jamus a matsayin mai bin Rasha sau- da-kafa, yayin da ya bukaci kasar da ta gaggauta inganta sha’abnin tsaronta a maimakon dogaro da Rasha.

Ana kallon taron na kwanaki biyu a matsayin mafi zafi da ba a taba ganin irinsa a cikin tsawon shekaru ba, in a bana Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka suka yi ta musayar kalamai mara dadi, yayin da shugaba Trump ya bukaci sauran kasashen NATO da su mayar wa Amurka da kudaden da ta kashe wajen samar da tsaro a yankin kasashen yammaci.

Sai dai tuni Uwargida Merkel ta mayar da martani ga Trump , in da ta ce, Jamus na da hurumin samar wa kanta da tsare-tsaren da ta ga dama, lamarin da ya sa shugabannin biyu suka yi musayar kalamai a wani zaman keke da keke a gefen taron na bana.

Taron na NATO na zuwa a yayin da ya rage kasa da mako guda shugaba Trump ya yi ganawarsa ta farko da shugaban Rasha, Vladimir Putin a birnin Heksinki.