Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Trump da Putin na ganawa a Helsinki

Shugabannin kasashen Amurka da Rasha sun bude ganawarsu mai cike da tarihi a birnin Helsinki na Finlad, in da Donald Trump ya yi alkawarin kulla dangantaka mai karfi tsakaninsa da Vladimir Putin.

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A cikin wani yanayi na rashin karsashi, shugabannin biyu sun yi musayar jawabin bude taronsu a gaban kafafen yada labarai, in da Putin ke cewa, lokaci ya yi na gudanar da muhimmiyar tattaunawa game da dangantakarsu da kuma bangarorin da suke samun sabani akai.

Shugaba Trump ya jinjina wa Putin kan rawar da gwamnatinsa ta taka wajen karbar bakwancin gasar cin kofin duniya wadda aka kammala a ranar Lahadin da ta gabata.

Trump ya ce, yana ganin suna da wata gagarumar dama a matsaynisu na kasashe, yayin da ya ce, sun shafe tsawon shekaru ba tare da mu’amala da juna ba.

Taron nasu zai mayar da hankali kan batun kwance damarar makamin nukiliya kamar yadda Trump ya bayyana, kuma ya ce, yana zaton duniya na fatan ganin sun dinke barakarsu lura da matsayinsu na manyan kasashen duniya masu karfin makamin nukiliya.

Trump na kokarin inganta dangantaka tsakaninsa da Putin ne duk da zarge-zargen da ake yi wa Rasha na kutse a siyasar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.