rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Rasha Zaben Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta tuhumi 'yar Rasha da leken asirin kasa

media
Maria Butina da aka tuhuma da leken asirin kasa a Amurka firenewsfeed.com

Gwamnatin Amurka ta tuhumi wata ‘yar Rasha da laifin leken asiri a madadin gwamnatin Rasha, in da ta kulla alakar kusanci da kungiyoyi siyasa na Amurka don samun bayanan sirri.


Kafafen yada labaran Amurka sun ce, Maria Butina ta kulla kyakkawar alaka da jam’iyar Republican,kuma ta zama mai rajin kare hakkin mallakar bindiga.

Sai dai tuhumar ba ta da alaka da binciken da ake gudanar kan zargin kutsen Rasha a zaben Amurka na 2016 da Donald Trump ya lashe.

Rahotanni na cewa, Butina na aiki ne a karkashin umarnin da take karba daga wani babban jami’in gwamnatin Rasha a Kremlin.

Sai dai Lauyan da ke kare Butina mai shekaru 29, Robert Driscoll ya ce, matar ba  jami’ar leken asiri ba ce, hasalima daliba ce a fannin ‘Siyasar Huladar Kasashen Duniya” kuma ta na fatan amfani da kwalinta na karatun digiri wajen gudanar da harkokin kasuwanci.