rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Rasha Zaben Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump na shan suka kan ganawarsa da Putin

media
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Leonhard Foeger

Ana ci gaba da sukar shugaban Amurka Donald Trump bayan ya kare Rasha daga zargin da ake yi ma ta na kutse a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a shekarar 2016.


Jim kadan da komawarsa gida a yammacin ranar Litinin daga Finland, Mr. Trump ya fara shan suka daga manyan Jami’an Musayar Bayanan Sirri na kasar da kuma jagororin Jam’iyyar Republican da suka bayyana ganawarsa da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin a matsayin abin kunya da kaskanci.

Sanata John McCain ya ce, ganawar ita ce mafi muni da wani shugaban Amurka ya taba yi a taihin kasar.

Kalaman Trump a yayin taronsa da Putin a Finland, sun saba da na Hukumomin Leken Asiri na Amurka, in da ya ce, Rasha ba ta da wani dililin shisshigi a zaben na 2016.

Kakakin Majalisar Amurka Paul Ryan ya ce, dole ne Trump ya fahimci cewa, “Rasha ba aminiyarsu ba ce”.

Wata sanarwa da Darektan Hukumar Musayar Bayanai ta Amurka, Dan Coats ya sanya wa hannu, ta zargi  Rasha da alhakin tabarbarewar demokradiyar Amurka, zargin da shugaba Putin ya musanta.

A ranar Litinin ne, shugabannin biyu suka shafe kusan sa’oi biyu suna tattaunawar keke da keke ba tare da mashawartansu ba a birnin Helsinki na Finland.