Isa ga babban shafi
EU-Google

EU ta ci Google tara mafi tsanani a tarihi

Kungiyar  Tarayyar Turai ta ci kamfanin Google tara mafi tsanani a tarihin kafuwar kamfanin da ta kai Euro bilyan hudu da milyan 340, lamarin da ake ganin zai kara tsamin dangantaka tsakanin Amurka da yankin Turai.

Kungiyar Tarayyar Turai ta zargi kamfanin Google da yaudarar masu amfani da manhajarsa don azurta kansa
Kungiyar Tarayyar Turai ta zargi kamfanin Google da yaudarar masu amfani da manhajarsa don azurta kansa REUTERS/Neil Hall
Talla

Kungiyar Turai ta sanar da wannan tara ce sakamakon abin da ta kira yin amfani da hanyoyin da suka saba wa ka’ida wajen sanya kangi da kuma takura wa jama’a da ke amfani da Android domin gudanar da bincike-bincike da sauran abubuwa da ke samar wa kamfanin makudan kudade.

Kwamishinar Sashen bai wa Kamfanoni damar yin gasa da juna a fagen kasuwanci a kungiyar ta Turai Margrethe Vestager, ta ce kamfanin da ke Amurka na cin ribar sama da Euro bilyan 95 a shekara ta hanyar tallace-tallace da ke bayyana lokacin da jama’a ke amfani da man hajarsa ta bincike dangin smartphones, to amma yana boye gaskiyar abin da yake samu.

Ko baya ga wannan tara ta Euro bilyan 4 da milyan 340 wadda ta kai kashi 10% na jarinsa, Kungiyar ta Turai ta kuma bukaci Google ya dakatar da wannan yaudara cikin kwanaki 90 ko kuma ya fuskanci sabbin matakai.

A 2017, kungiyar ta samu kamfanin da laifi, in da ta dora masa biyan tarar Euro bilyan 2 da milyan 400, to sai dai a wannan karo kamfanin na Google ya ce zai daukaka kara a game da wannan tara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.