Isa ga babban shafi
Syria

Fararen hula da dama sun mutu a yankin Golan na Syria

Kungiyar dake sa ido kan rikicin kasar Syria tace wani harin sama da dakarun gwamnatin kasar suka kai kusa da tuddun Golan sun yi sanadiyar kashe fararen hula da dama. 

Yankin Golan da dakarun  Syria suka kai farmaki zuwa yan tawaye
Yankin Golan da dakarun Syria suka kai farmaki zuwa yan tawaye JALAA MAREY / AFP
Talla

Shugaban kungiyar Rami AbdelRahman yace tun ranar lahadi dakarun gwamnati ke cigaba da ruwan wuta a yankin da ya hada da kauyen Ain al-Tina dake kusa da iyakar Deraa.

Kungiyar tace mutane 14 aka kashe cikin su har da yara kanana 5.

A yan watanni da suka gabata,Majalisar Dinkin Duniya na cigaba da sa matsin lamba kan Rasha, domin ta samar da hanyoyin kawo karshen farmaki daga dakarun shugaba Assad a kudancin Syria, wacce ke fuskantar lugudan wuta daga dakarun gwamnatin shugaba Bashar Al-Assad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.