Isa ga babban shafi
South Africa

Mandela ya yi tasiri a rayuwata- Barack Obama

Kasar Afrika ta Kudu na bikin cika shekaru 100 da haihuwar marigayi Nelson Mandela da ake kallo a matsayin gwarzon yaki da wariyar launin fata, in da tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya jagoranci wani taron karfafa wa matasa guiwar shiga harkokin shugabanci.

Toshon shugaban Amurka  Barack Obama a bikin tunawa da Nelson Mandela a birnin Johannesburg da ke Afrika ta Kudu
Toshon shugaban Amurka Barack Obama a bikin tunawa da Nelson Mandela a birnin Johannesburg da ke Afrika ta Kudu REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

A kowacce ranar 18 ga watan Juli ake bikin tunawa da Mandela a sassan duniya ta hanyar gudanar da ayyukan taimako, yayin da gidauniyar Nelson Mandela ta bukaci al’umma da su yunkura wajen kawo sauyi da sunan marigayin.

Obama ya shaida wa dandazon matasa 200 da suka halarci taron sanin makamin shugabanci a birnin Johannesburg cewa, Mandela na a matsayin babban gwarzon da ya yi tasiri a rayuwarsa.

A yayin gabatar da jawabi Obama ya yi barkwaci, in da yake cewa, “ da dama daga cikin mutane na daukan Mandela a matsayin tsohon da ke da furfurar kai kamar tawa.”

“Abinda yawancin mutanen duniya ba su fahimta ba shi ne, Mandela ya fara gwagwarmaya ne tun yana matashi da zimmar samar wa kasarsa ‘yanci. Wannan ya yi tasiri a rayuwata” In ji Obama.

Shi ma Archbishop Desmond Tutu mai shekaru 86 ya tuna Mandela da irin gwagwarmayar da suka yi tare game da yaki da mulkin mallaka na turawa.

Tutu ya ce, “babban abin da ya banbanta Mandela da mutane shi ne saukin kansa. Shi wani kyakkyawan misali ne a zamantakewar dan adam.”

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.