Isra'ila ta bayyana yankinta a matsayin kasar Yahudawa zalla
Majalisar Israila ta amince da wata doka mai sarkakiya wadda ta bayyana yankin kasar a matsayin kasar Yahudawa zalla, sabanin kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.
Wallafawa ranar:
‘Yan majalisun Israila 62 suka amince da wannan sabuwar doka mai sarkakiya, yayin da 55 suka kada kuri’ar kin amincewa da ita.
A karkashin wannan sabuwar doka, kasar ta Yahudu zata janye harshen larabci a matsayin harshen hukuma da kuma mayar da gina gidajen Yahudawa Yan kama wuri zauna a matsayin bukatar kasa.
Sabuwar dokar ta kuma bayyana Birnin Kudus a matsayin daukacin Babban Birnin Israila, sabanin yadda kasashen duniya ke bukatar ganin sun raba tare da Falasdinawa.
Yan Majalisu Larabawa dake Majalisar sun yi Allah wadai da matakin, yayin da Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana shi a matsayin kwakwaran mataki.
Wannan mataki zai ci karo da duk wani yunkuri na kasashen duniya da kuma Majalisar Dinkin Duniya na sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu