rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka China Rasha Majalisar Dinkin Duniya Korea ta Arewa Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Takunkumai za su ci gaba da aiki kan Korea ta Arewa - Amurka

media
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo tare da babban sakataren Majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, a Hedikwatar Majalisar da ke birnin New York. 20 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Brendan McDermid

Amurka ta bukaci kasashen China da Rasha, da kuma sauran kasashen duniya, su ci gaba da mutunta takunkuman karya tattalin arzikin da aka kakabawa Korea ta Arewa, har sai kasar ta cika alkawarin da ta dauka, na lalata ilahirin makaman nukiliyar da ta mallaka.


Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da jakadiyar kasar a Zauren majalisar dinkin duniya Nikki Haley sukai wannan kira, bayan gabatar da jawabi a zauren kwamitin tsaron majalisar.

Kiran da Amurka ta yin a cigaba da tsaurara takukumanm da aka kakabawa Korea ta Arewa, ya biyo bayan, kudirin da kasashen Rasha da China suka gabatar, na neman a tattauna kan yiwuwar dage takunkuman.

A makon da ya gabata ne Amurka ta gabatarwa zauren kwamitin Tsaro na majalisar dinkin duniya korafin cewa, duk da takunkuman hana saidawa Korea ta Arewa man fetur, daga farkon wannan shekara zuwa 30 ga watan Mayu, Korea ta Arewan ta yi fasakaurin man fetur cike a akalla manyan jiragen ruwa 89.