Isa ga babban shafi
China-Amurka

China ta mayar da martini kan zargin Trump na cogen kudi ga Amurka

Kasar China ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi kanta na cewa ta na yin coge a harkar musayar kudade don ganin darajar takaddar kudin Dala ta Amurkan ta sauka.Martinin na China na zuwa ne a dai dai lokacin da yakin kasuwanci ke kara tsananta tsakanin Donald Trump na Amurka da takwarinsa na China Xi Jinping.

Tuni dai batun ya shiga gaban hukumar kasuwanci ta duniya wadda ta nemi sasantawa tsakanin kasashen biyu don dai daita harkokin kasuwancin da ke tsakaninsu.
Tuni dai batun ya shiga gaban hukumar kasuwanci ta duniya wadda ta nemi sasantawa tsakanin kasashen biyu don dai daita harkokin kasuwancin da ke tsakaninsu. 路透社
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen China ta ce kasar ba ta da nufin cutar da kowacce kasa musamman a batun da ya shafi musayar takaddar kudi, maimakon haka ta fi mayar da hankali kan kasuwancinta da kasashen duniya.

A juma’ar da ta gabata ne shugaba Trump na Amurka ya bankado cewa China da kasashen tarayyar Turai na yin kumbiya-kumbiya a bangaren musayar kudade yayin cinikayya da Amurka da nufin cutar da kasar tare da dankwafar da darajar takaddar kudin kasar ta dala.

Amurkan da China wadanda ke matsayin mafiya karfin tattalin arziki a nahiyoyinsu, sun fada yakin kasuwanci ne tun bayan da Trump na Amurka ya kakaba haraji kan kayan dala biliyan 34 da Chinan ke shigarwa yayinda ya kara daukar aniyar kara harajin kan wasu nau’in kayan dala biliyan 200 na Chinan ko da dai a wannan karon ta ce bazata ta kyale ba.

Tuni dai batun ya shiga gaban hukumar kasuwanci ta duniya wadda ta nemi sasantawa tsakanin kasashen biyu don dai daita harkokin kasuwancin da ke tsakaninsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.