Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

An fara taron kasa da kasa kan yaki da cutar HIV Aids

Yau aka fara taron kasa da kasa kan yaki cutar HIV-AIDs ko SIDA wacce ke karya garkuwar jiki da ke samun halartar wakilai daga sassa daban daban a Duniya, taron wadda ke gudana a birnin Amsterdam na kasar Holland.

Taron na birnin Amsterdam da ke samun halartar fitattun mutane ciki har da Bill Clinton da Yarima Harry zai kara karfafa matakan ceton rayukan jama'a daga halaka daga annobar.
Taron na birnin Amsterdam da ke samun halartar fitattun mutane ciki har da Bill Clinton da Yarima Harry zai kara karfafa matakan ceton rayukan jama'a daga halaka daga annobar. 照片来源:路透社 REUTERS/Yves Herman
Talla

Cikin mahalarta taron, har da tsohon shugaban Amurka Bill Clinton, da Yerima Harry na Ingila da kuma mawakin nan Elton John wadanda dama dukkaninsu na cikin masu fafutukar ganin an inganta rayuwar masu fama da cutar tare da wayar da kai don kawo karshenta a doron kasa.

Taken taron na bana wanda shi ne karo na 22 shi ne ''Kawar da kyama da karfafa kaunar Juna" wanda ke nuna bukatar rage kyamar masu fama da wannan cuta ta HIV Aids tare da karfafa musu gwiwar samun rayuwa mai inganci.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da cutar ta Aids na fatan ganin bayan annobar nan da shekarar 2030, wacce kuma ta bayyana fargaba kan yadda cutar ke kara yaduwa a wasu kasashen duniya.

Alkaluman majalisar na nuni da cewa, mutum miliyan daya da dari takwas ne suka kamu da cutar a bara, a yayin da mutum akalla miliyan 37, yanzu haka ke dauke da kwayar cutar a sassan duniya.

Taron na birnin Amsterdam zai kara karfafa matakan ceton rayukan jama'a daga halaka daga annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.