Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

Isra'ila ta bude hanyar Gaza da ta datse

Kasar Isra’ila za ta bude hanyar shigar da kayayyaki zuwa zirin Gaza muddin zaman lafiya ya dore bayan cimma matsayar tsagaita musayar wuta tsakanin Yahudawa da Falasdinawa. Tun a ranar 9 ga wannan wata na Juli ne, Isra’ila ta kulle hanyar a matsayin martani ga hare-haren Falasdinawa.

Hanyar Kerem Shalom da Isra'ila ta datse a farko don hana shigar da kayayyaki zuwa yankin Zirin Gaza
Hanyar Kerem Shalom da Isra'ila ta datse a farko don hana shigar da kayayyaki zuwa yankin Zirin Gaza SAID KHATIB / AFP
Talla

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gargadi cewa, dakarun kasar na cikin shirin ko takwana don kaddamar da hare-hare a zirin Gaza, matukar bukatan hakan ya tazo bayan kazancewar rikici tsakanin bangarorin biyu a ranar Jumma’a.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, zirin na Gaza na fuskantar mummunar matsalar karancin man fetir, lamarin da ke illa ga ayyukan asibitoci da samar da ruwan sha, abin da ya sa Majalisar ta bukaci Isra’ila da ta gaggauta janye matakinta na dates hanyar.

Sai dai a ranar Lahadi, ministan tsaron Isra’ila, Avigdor Lieberman ya bada tabbacin sake bude wannan hanyar ta shigar da kayayyakin zuwa Gaza da ake kira Kerem Shalom.

Ministan ya ce, matukar zaman lafiya ya dore nan da ranar Talata, to babu shakka za a ci gaba da gudanar da harkoki a Kerem Shalom kamar yadda aka saba a baya.

Isra’ila ta dauki matakin ne saboda yadda Falasdinawan Hamas suka dauki watanni suna amfani da Filfilwa da Balan-Balan wajen aika wutar Aci bal-bal cikin lardin Isra’ila, lamarin da ya haddasa ma ta gagarumar asara musamman a filayen gonakinta.

Yanzu haka dai, kasar ta Isra’ila na bukatar Falasdinawan da su kawo karshen wannan harin, yayin da bangarorin biyu suka cimma matsayar tsagaita wuta a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.