Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Trump da Rouhani na yakin cacar-baka

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Iran, Hassan Rouhani sun yi musayar zafafan kalamai a dai dai lokacin da zaman dari-dari ke ci gaba da tsananta tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Matej Leskovsek
Talla

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi kasar Iran da ta kauce wa duk wani yunkurin yi wa kasar Amurka barazana, ko kuwa ta gamu da fushin da kasashen kalilan ne suka gamu da irinsa a tarihin duniya.

A wani sakon Twitter da ya aikewa shugaba Rouhani , Trump ya shaida wa Iran cewar, Amurka ba za ta ci gaba da zama kasar da ake yi wa barazanar tashin hankali da kuma kisa ba.

Gabanin martanin Trump, shugaban Iran ya gargadi takwaran nasa da ya kauce wa wasa da jelar zaki, in da ya ce, rikici da Iran zai kasance musabbabin dukkanin yake-yake.

Wannan sabuwar cacar-bakarn na zuwa ne kwanaki uku bayan wani jami’in shugaban na Iran ya bayyana cewar, sau 8 shugaba Trump ya nemi ganawa da shugaba Rouhani lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya a bara, amma shugaban na Iran ya ki.

A cikin watan Mayun da ya gabata ne, shugaba Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya da suka hada da Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha da kuma China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.