Isa ga babban shafi
EU-Amurka

EU za ta kakaba wa Amurka harajin Dala biliyan 20

Kungiyar Kasashen Turai ta yi barazanar kakaba wa Amurka harajin Dala biliyan 20 kan kayan da kasar ke sarrafawa a matsayin ramako kan yadda Amurkar ta dora wa motocin da ake kerawa a Turai sabbin kudaden haraji.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, Tarayyar Turai na kwarar Amurka dangane da batun haraji.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, Tarayyar Turai na kwarar Amurka dangane da batun haraji. 路透社。
Talla

Ministar  Kasuwanci na Turai, Cecilia Malmstrom ta bayyana haka gabanin ganawar da ake shirin yi tsakanin shugaba Donald Trump da shugaban Kungiyar Turai Jean-Claude Juncker a Washington.

Mlmstrom ta ce, ba sa fatan  aiwatar da yarjejeniyar saboda fatansu na ganin an cimma masalaha, amma kuma idan hakan yaci tura, babu yadda za su yi illa aiwatar da matakin.

Kayayyakin da harajin zai shafa daga Amurka sun hada da injinan kayan noma da na masana’antu da ke zama a matsayin martani kan shirin shugaba Trump na sanya haraji kan motoci da kuma kayan gyaransu.

Shugaba Trump ya bayyana kasashen Turai a matsayin wadanda ke kwarar Amurka, in da yake cewa yana daukan wannan matakin ne domin taimaka wa jama’ar kasarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.