rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ukraine Rasha Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EU ta sanya karin takunkumai kan Rasha

media
Shugaban kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker. REUTERS/Joshua Roberts

tarayyar turai ta EU ta kara fadada takunkuman da ta sanya kan Rasha ciki har da kamfanonin da suka taimaka wajen gina babbar gadar da ta hade kasar da yankin Crimea da ta mamaye wadda a cewar kungiyar hakan ya keta dokar mulki na kasar Ukraine.


A cewar sanarwar da Kungiyar EU ta fitar ta ce akalla kamfanoni da ma’aikatu shida da shugaba Vladimir Putin na kasar ya kaddamar a watan Mayu ne za’a kwace kaddarorinsu bisa ga rawar da suka taka wajen gina babbar gadar da ta hada yankin Crimea da Kasar ta Rasha wacce aka yi ba bisa ka’ida ba cikin jerin takunkumanta.

Biyu daga cikin kamfanoni da ma’aikatun da aka fitar da sunayen su na karkashin ikon dan kasuwa Arkady Rotenberg makusanci ga shugaba Putin

Haka zalika kungiyar ta EU ta fitar da jerin takunkumai da ta sanya kan rasha saboda rawar da take takawa wajen ta da rikici a gabashin Ukraine.

Jimilar kamfanoni 44 ne yanzu haka ke fuskantar takunkuman na EU akan Rasha.

Akwai kuma kari Wasu mutane 155 ciki har da wadanda ke da halakar kusanci da Putin suma aka kwace kaddarorinsu tare hana su tafiye tafiye zuwa wasu kasashen.