Isa ga babban shafi
Venezuela

Shugaba Maduro ya ketare rijaya da baya

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya ketare rijaya da baya, bayan da wasu kuramen jirage dauke da bama-bamai suka yi kokarin halaka shi a lokacin da yake jawabi zuwa sojojin kasar a Caracas.

Nicolas Maduro a lokacin harin da aka kai masa a birnin Caracas na kasar Venezuela
Nicolas Maduro a lokacin harin da aka kai masa a birnin Caracas na kasar Venezuela VENEZUELAN GOVERNMENT TV/Handout via REUTERS TV
Talla

Yan lokuta bayan samun kan sa, Shugaban kaar ta Venezuela Nicolas Maduro ya zargi wasu manyan jami’an kasar dake zaune a Amurka da kokarin kifar da gwamnatin sa, Maduro ya kuma zargi Shugaban Colombia Juan Manuel Santos da hannu a harin.

Kasar Venezuela ta fada rikicin siyasa kama daga shekarar da ta 2017, bayan zaben yan majalisu da ga baki daya ake zargi da kasancewa yan amshi shatar Shugaban kasar.

A wannan hari mutane 7 daga cikin mau tsaron Shugaban kasar ne suka samu rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.