rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Muhalli Kimiya Canjin Yanayi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Ci gaba da amfani da man fetur hadari ne babba ga muhalli"

media
Kauyen Badswat da ke fuskantar nutsewa cikin ambaliyar ruwa, sakamakon narkewar katafariyar kankarar lardin Gilgit-Baltistan a kasar Pakistan. 27 ga watan Yuli, 2018. Reuters/Peer Muhammad

Wani Binciken masana yanayi ya bayyana bukatar kawo karshen amfani da man fetur, da kuma rungumar sabbin dabarun samun makamashi domin kawo karshen yadda ake gurbata muhalli, da kuma samun yanayi mai zafi a duniya.


Masanan sun ce, muddin aka cigaba da narkar da kankarar dake samar da sanyi da kuma kona daji kana da fitar da hayakin dake gurbatamuhalli kamar yadda akeyi kowacce shekara, duniya zata fuskancin matsalar da bata taba gani ba wajen samun zafi.

Masanan daga Jami’ar Copenhagen da Jami’ar Australia da kuma Cibiyar gudanar da binciken yanayi dake Jamus duniya na fuskantar barazanar samun munanan ambaliya, da kuma ruwa da iskar dake illa ga jama’a nan da shekaru maus zuwa.