Isa ga babban shafi

A shirye nake na cimma sabuwar yarjejeniya kan nukiliyar Iran - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce a shirye yake, ya tattaunawa da gwamnatin Iran, don cimma sabuwar yarjejeniya kan shirin nukiliyar kasar.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Trump ya yi wannan tayi ne, a dai dai lokacin da ya ke sanar da fara aikin takunkuman da Amurka ta maida kan kasar ta Iran, wadanda aka janye a baya.

A daren ranar Litinin 6 ga watan Agusta, 2018, kashin farko na takunkuman da Trump ya maida kan Iran suka soma aiki, wadanda za su shafi, haramta musayar kudin dala da kasar, da kuma haramta mata cinikayya da wasu masana’antun Amurka da suka hada da na kera motoci da kuma darduma.

A ranar 5 ga watan Nuwamba kuma takunkuman kashi na biyu, za su soma aiki, wandanda za su haramtawa Iran saidawa kasashen duniya man da take hakowa, matakin da ba shakka zai yi tasirin gurgunta tattalin arzikinta, to sai dai kasashen China, India da Turkiya sun ce ba zasu yanke baki dayan huldar cinikayyar da ke tsakaninsu da kasar ta Iran ba.

A watan Mayu da ya gabata, shugaba Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukilyar Iran da kasashen duniya suka yi a shekarar 2015, bisa dalilan cewa tilas sai yarjejeniya ta dakile shirin Iran na kera manyan makamai masu linzami da kuma rage tasirinta a muhimman al’amuran yankin gabas ta tsakiya, musamman tsaro.

Sai dai yayin da ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ke maida martani kan tayin na Amurka, ya ce abu ne mai wahala, tattaunawa tsakaninsu da Trump ta yiwu, la’akari da yadda ya yi watsi da yarjejeniyar nukiliyar ta farko ba tare da ya mutunta ta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.