rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Rasha Zaben Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump bai musanta ganawar da dansa ya yi da Rasha ba

media
Shugaban Amurka Donald Trump tare da dansa Donald Trump Jr REUTERS/Mike Segar/

Shugaban Amurka Donald Trump ya amince cewar, dansa ya gana da wata lauya 'yar kasar Rasha a gininsa na Trump Tower domin samun bayanai kan 'yan adawarsa gabanin zaben shekarar 2016 da ya ba shi nasara kan uwargida Hillary Clinton.

 


Wannan ne karo na farko da shugaba Trump ke amsa ganawa da mutanen kasar Rasha wadda ake zargi da katsalandan a zaben na Amurka, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan kutsen na Rasha a zaben.

Shugaba Trump ya ce, ganawar tsakanin dansa da Lauya, Natalia Vaselnitskaya bai saba ka'ida ba kuma a cewarsa,an yi ganawar ce domin samun bayanai kan abokin hamayya, kuma hakan ba wani sabon abu ba ne.

Dan shugaba Trumnp ya shaida wa jaridar New York Times a shekarar da ta gabata cewar, an yi ganawar ce saboda shirin karbar yara marayu daga Rasha domin samar musu da wurin zama a Amurka.

Suma lauyoyin shugaba Trump sun ce, babu saba ka’ida kan ganawar tsakanin bangarorin biyu.