rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka China Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta kaddamar da sojin sararin samaniya

media
Rundunar Kare Sararin Samaniyar Amurka za ta taka rawa wajen tinkarar hare-haren da ka iya kunno kai daga sararin samaniya da kuma Sahara Tech. Sgt. Kamaile Casillas/Pacific Air Forces/DVIDS/Handout via

Gwamnatin Amurka ta kaddamar da shirinta na samar da rundunar sojin kare sararin samaniya wadda za ta kasance daya daga cikin rassa shida na dakarun kasar. Mataimakin shugaban kasar, Mike Pence ya ce, lokaci ya yi na kintsawa don tinkarar fagen daga.


A cikin watan Yunin da ya gabata ne shugaban Amurka Donald Trump ya umarci kafa rundunar, in da ya ce, ma’aikatar tsaro ta Pentagon na bukatar wannan runduna don tinkarar hare-haren da ka iya kunno kai daga sararin samaniya da kuma saharar Amurka.

Sai dai kafuwar rundunar na bukatar amincewar Majalisaun Dokoki kasar, yayin da tuni wasu mabobin majalisun da manyan hafsoshi suka fara nuna shakku game da samuwarta musamman ganin irin tarin dukiyar da shirin zai lakume baya ga matakan da za a bi.

Sai dai mataimakin shugaban na Amurka, Mike Pence ya bayyana aniyar gwamnatin kasar karara ta samar da rundunar nan da shekarar 2020, wato locakin cikar wa’adin shugaba Trump akan karaga.

Mr. Pence ya ce, za a yi amfani da kwararru da jaruman sojoji wajen kafa rundunar wadda za ta kare da  kuma murkushe sabbin barazanar da Amurukawa ke fuskanta.

A cewar Pence, wannan rundunar na da matukar muhimmanci don tinkarar Rasha da China da ke aiki tukuru wajen daukan matakan dakushe karsashin tauraron dan Adam.