rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Turkiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya kara haraji kan karafan da Turkiya ke kai wa Amurka

media
Matakin na Trump na zuwa ne a dai dai lokacin da alaka ke kara tsami tsakanin Turkiyyan da Amurka. Rick Loomis/Getty Images/AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewar ya ribanya haraji akan karafa da kuma gorar ruwan dake zuwa daga Turkiya, a wani mataki da ake ganin zai kara jefa kasar cikin mawuyacin hali.


A sakon da ya aike ta kafar twitter, shugaba Trump ya ce sakamakon faduwar darajar kudin Turkiya na Lira, ya ribanya musu haraji akan wadannan kayayaki, saboda yadda dalar Amurka ke kara daraja.

Shugaba Trump ya bayyana cewar dangantakar da ke tsakanin Amurka da Turkiya yanzu haka bata da kyau.

A bangare daya, shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bukaci al’ummar kasar da su sayar da kudin su na dala domin sayen kudin gida dan ganin an daga darajar Lira.

Ana dai ci gaba da fuskantar banbancin ra'ayi a batutuwa da dama tsakanin Amurkan da Turkiyya musamman a al'amura masu alaka da rikicin kasar Syria dama batun mayar da kudus babban birnin Isra'ila sai kuma batu na baya-bayan sabon takunkuman Iran.