rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Kimiya Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

NASA za ta kaddamar da kumbon da zai kusanci Rana

media
Kumbon da hukumar NASA ta kaddamar da zai gudanar da bincike kan sirrikan duniyar Rana, jihar Florida, Amurka. 8 ga watan Agusta, 2018. Courtesy Bill Ingalls/NASA/Handout via REUTERS

Cibiyar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA, za ta kaddamar da kumbonta da aka kera kan dala biliyan daya da rabi, da zai zama na farko da ya kai ga duniyar Rana.


Kumbon wanda NASA za ta harba shi zuwa zuwa sama daga jihar Florida a yau Asabar, zai gudanar da bincike ne kan wasu sirrika na tsakiyar rana, da ake kira da 'Corona', wanda masana sukai ittifakin, zafinsa ya ninka na wajen rana sau 300.

Kumbon wanda aka sanyawa suna The Parker Solar Probe zai kuma taimaka masana sararin samaniya da ke duniya, wajen hasashen lokacin da kakkarfar guguwar da ke tsananin gudu a zagayen rana ka iya ketowa doron duniya.

Kumbon dai gina shi da kaurin inchi hudu da rabi, da ke karfin bashi kariya daga karfin zafin rana mafi tsanani da ake ji a doron duniya da ya ninka sau 500, wato kwankwacin zafin digiri 1, 371 a ma’aunin Celcsius.

Ana sa ran da zarar kumbon ya kusanci Rana, gudunsa zai karu zuwa saurin tafiyar kilomita dubu 700, 000 cikin awa guda, abin da zai bashi damar zama abin da dan adam ya kera mafi sauri a tarihi.