rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Syria Sudan ta Kudu Afghanistan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An tsananta hare-hare kan jami'an agaji a kasashen duniya

media
Wasu jami'an agaji a Syria na kan aikin ceto ABDULMONAM EASSA / AFP

Wani bincike ya nuna cewar an samu karuwar hare-haren da ake kai wa jami’an aikin agaji, in da a bara kawai aka kashe kusan 140, adadin da ya zarce wanda aka gani a shekarar 2016 da kashi 23.


Wadannan alkaluma da hukumar bincike mai zaman kanta ta gabatar bayan nazari kan kungiyoyin da ke gudanar da aikin agaji a duniya, sun bayyana yadda aka samu karuwar kai hari kan jami’an aikin agaji da garkuwa da su da kuma kisa a kasar Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Rahotan ya bayyana cewar kasashen Sudan ta Kudu da Syria da Afghanistan da kuma Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya suka fi hadari wajen gudanar da aiki, ganin yadda aka samu kashi biyu bisa uku na ire-iren wadannan munanan hare-hare 158 da aka kai bara.

Alkaluman binciken sun ce, an kai hari sau 313 kan jami’an aikin agaji a kasashe 22, kuma an kashe 139 daga cikinsu, yayin da aka raunana 102, kana aka yi garkuwa da 76, in da daga bisani aka kashe 4.

Abby Stoddard da ya jagoranci binciken, ya ce duk da yake adadin hare-haren na tsakanin shekarar 2016 da bara kusan daya ne, amma mutanen da aka kashe bara sun zarce na shekarar da ta gabace ta.

Shugaban hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, Jan Egeland ya bukaci hukunta wadanda ake zargi da hannu a hare-haren.