Isa ga babban shafi
Yemen

Yaran da Saudiya ta kashe a Yemen sun kai 40

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta ce, kananan yara 40 aka kashe a wani hari da rundunar hadaka da Saudiya ke jagoranta ta kai kan wata motar safa a arewacin Yemen, alkaluman da suka ninka wadanda kungiyar ta fitar a baya.

Dubban 'yan kasar Yemen sun yi zanga-zangar nuna adawa da kisan kananan yaran 'yan makaranta
Dubban 'yan kasar Yemen sun yi zanga-zangar nuna adawa da kisan kananan yaran 'yan makaranta REUTERS/Naif Rahma
Talla

Fitar da sabbin alkaluman na zuwa ne bayan gudanar da jana’izar kananan yaran 'yan makaranta a ranar Litinin a makabartar lardin Saada da ke karkashin ikon 'yan tawayen Houthi.

Dubban ‘yan kasar Yemen sun nuna bacin ransu kan Saudiya da Amurka a yayin gudanar da jana’izar yaran.

Mahalarta jana’izar sun yi ta daga hotunan yaran da aka kashe da kuma furta munanan kalamai kan Saudiya da Amurka.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci gudanar da sahishin bincike kan kazamin harin na ranar Alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.