Isa ga babban shafi
Venezuela

An kama babban soja kan zargin yunkurin kisan Maduro

Jami’an tsaron Venezuela sun kama wani babban Manjon soji kan zargin sa da hannu a yunkurin kisan shugaban kasar Nicolas Maduro. Kawo yanzu akalla mutane 14 gwamnatin kasar ta kama tare da gurfanar da su gaban kotu don amsa zargin yunkurin kisan shugaban.

Venezuela, Nicolas Maduro da ya tsallake rijiya da baya
Venezuela, Nicolas Maduro da ya tsallake rijiya da baya Miraflores Palace
Talla

A cewar babban mai shigar da kara na Venezuela, Tarek William Saab za su ci gaba da kama duk wanda suke zargin yana da hannu a yunkurin kisan shugaban, tare da gurfanar da su gaban kotu har zuwa lokacin da za a kama tare da hukunta masu shirin kashe shugaban.

Hukumomin na Venezuela sun gurfanar da shugaban rundunar tsaron kasar Manjo Janar Alejandro Perez Gomez gaban kotu tare fitaccen dan siyasa Juan Requesens don amsa zargin da ake musu na kitsa yadda aka kai harin na ranar 4 ga watan Agusta wanda bai yi nasara ba.

Ya zuwa yanzu dai akalla mutane 14 hukumomin na Venezuela suka gurfanar gaban kotu kan zargin kitsa harin ko da dai a bangare guda shugaba Maduro na dora alhakin harin kan wani dan kasar mazaunin birnin Floridan Amurka, Osman Delgado Tabosky da ya yi gudun hijira daga kasar.

A karshen makon da ya gabata, kai tsaye shugaba Maduro ya fito ya bayyana goyon bayansa ga tayin da Amurka ta yi na gudanar da bincike a Floridan don gano wadanda suka kitsa harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.