Dorina mafi tsufa a duniya ta mutu a birnin Kudus
Dorina mafi tsufa a duniya da ke tsare a gidan ajiye dabbobin dawa na Biblical Zoo da ke birnin Kudus ta mutu tana da shekaru 59 da haihuwa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Masu kula da gidan dabbobin na Biblical da aka samar tun shekarar 1939 sun ce, dorinar mai suna Tami ta mutu ne a yayin da take barci a cikin wani tafki da ake tsare da ita a ranar Alhamis.
Daya daga cikin ma’aikatan gidan dabbobin ya shaida wa jaridar Hayom ta Isra’ila cewa, suna cikin mawuyacin hali sakamakon mutuwar Tami.
A shekarar 2017 ne wata dorina mai suna Bertha ta mutu a birnin Manila na kasar Philippines bayan ta shafe shekaru 65 a raye, kuma ita ce mafi tsufa a wancan lokacin da ke tsare a wani gidan ajiyar dabbobi.
Bayanai na nuna cewa, dorina ka iya rayuwa har tsawon shekaru 40 zuwa 50.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu