Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya-Isra'ila

Isra'ila ta yi watsi da kudirin kare Falasdinawa

Isra’ila ta yi watsi da rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ke gabatar da wasu kudurori 4 da za a yi amfani da su wajen bai wa Falasdinawa kariya, daga cin zarafin da Isra’ilan ke musu.

A cewar Isra'ilan babu wani kudurin kare Falasdinawa da zai yi amfani matukar ba ita ta samar da shi ba.
A cewar Isra'ilan babu wani kudurin kare Falasdinawa da zai yi amfani matukar ba ita ta samar da shi ba. REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

A cewar Jakadan Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya babu wani kudirin kare Falasdinawa da zai yi amfani face idan daga garesu ya ke, yana mai cewa maimakon bata lokaci wajen gabatar da kudirorin kamata ya yi majalisar ta gargadi shugabannin Falasdinawa kan su dauki matakan kare al’ummarsu daga jefa kansu cikin hadari.

Kudurorin da Majalisar ta gabatar cikin wani rahoto da Antonio Gutteress ya fitar na da nufin kawo karshen gallazawar da Isra’ilan ke wa Falsdinawa ta hanyar tura dakarun majalisar dinkin duniya domin bai wa falasdinawan kariya daga sojin isra’ila da kuma neman amincewar kwamitin tsaron majalisar wajen samar da rundunar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.