Isa ga babban shafi
Amurka-Korea ta Arewa

Amurka ta nada manzo na musamman game da Korea ta arewa

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya sanar da sunan Stephen Biegun a matsayin jakada na musamman mai shiga tsakani a tattaunawar Korea ta Arewa da Amurka.Mr Stephen wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban kamfanin motoci na Ford, a mako mai zuwa ne zai ziyarci Korea ta Arewan bisa rakiyar Mr Pompeo.

A watan Yunin da ya gabata ne Shugaba Kim Jong Un da takwaransa na Amurka Donald Trump suka yi wata ganawa ta musamman a Singapore wadda Trump ya kira da mai matukar tarihi la’akari da yadda kasashen biyu suka dau lokaci suna takun saka.
A watan Yunin da ya gabata ne Shugaba Kim Jong Un da takwaransa na Amurka Donald Trump suka yi wata ganawa ta musamman a Singapore wadda Trump ya kira da mai matukar tarihi la’akari da yadda kasashen biyu suka dau lokaci suna takun saka. Reuters/路透社
Talla

Nadin wanda Mike Pompeo ya sanar da shi a yau, wani mataki ne da ke nuna yadda Amurka ta dauki batun tattaunawar da Korea ta Arewa da muhimmanci inda a mako mai zuwa Mr Stephen Biegun mai shekaru 55 zai isa Pyongyang bisa rakiyar Mike Pompeo sakataren harkokin wajen Amurka.

Stephen wanda nadin na shi a matsayin mai shiga tsakani kan tattaunawar ta Amurka da Korea ke nufin cewa zai rika sanar da Washington halin da ake ciki kan shirin kwance makaman nukiliyar na Korea ta Arewa.

Ziyarar ta Pompeo tare da Mr Stephen zuwa Korea ta Arewan a mako mai zuwa zai zamo karo na hudu da Mr Pompeo ke kai ziyara kasar tun bayan ganawar Kim da Trump.

A watan Yunin da ya gabata ne Shugaba Kim Jong Un da takwaransa na Amurka Donald Trump suka yi wata ganawa ta musamman a Singapore wadda Trump ya kira da mai matukar tarihi la’akari da yadda kasashen biyu suka dau lokaci suna takun saka.

Yayin waccan ganawa, Kim ya sha alwashin kwance makaman nukiliyar da ya mallaka ko da dai kawo yanzu babu tabbacin ko ya fara aikin kwancewar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.