Isa ga babban shafi
Amurka-Trump

Tsige ni daga mulki zai rugurguza tattalin arzikin Amurka - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa, tattalin arzikin Amurka zai ruguje muddin aka yi gangancin tsige shi daga shugabancin kasar. Trump ya yi gargadin ne yayin ganawa da manema labarai dangane da nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannin bunkasa tattalin arzikin Amurka.

Shugaban na Amurka Donald Trump ya ce matukar aka yi yunkurin sauke shi akwai babban barazana ga tattalin arziki kasar da ya ke ta kokarin ganin ya kara bunkasa shi a yanzu.
Shugaban na Amurka Donald Trump ya ce matukar aka yi yunkurin sauke shi akwai babban barazana ga tattalin arziki kasar da ya ke ta kokarin ganin ya kara bunkasa shi a yanzu. Rick Loomis/Getty Images/AFP
Talla

Gargadin da Trump ya yi dangane da hadarin tsige shi daga shugabancin Amurka, da ya ce zai haddasa rushewar tattalin arzikin kasar, ya zo a dai dai lokacin wasu masu fashin baki kan siyasar Amurka da matakin kasa da kasa suka bayyana cewa, shugabancinsa na fuskantar hadarin yiwuwar a kawar da shi ta hanyar tsigewa.

Yayin zantawar ta sa da kafar yada labaran Fox, Donald Trump ya kuma yi dirar mikiya kan ministansa na shari’a Jeff Sessions wanda ya soka da kakkausan harshe bisa zarginsa da nuna gazawa a cikin aikinsa, musamman kasa iya kare manufofin gwamnatinsa.

Wannan dambarwa dai na zuwa ne kwanaki kada bayan tsohon lauyan shugaban na Amurka Micheal Cohen ya shaidawa kotun kasar cewa ya aikata laifin biyan wasu mata kudade ba bisa ka’ida domin hana su fallasa alakar assha da ke tsakaninsu, wanda ya ce Trump din ne ya bashi umarnin yin hakan don kare kimarsa a siyasance wajen samun nasarar lashe zaben shugaban kasa, matakin da ya sabawa dokokin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.