Isa ga babban shafi
Venezuela

Talauci na tilasta wa 'yan Venezuela tserewa

Alkaluma na cewa dubban mutane na tserewa daga Venezuela domin neman mafaka a wasu kasashen ketare sakamakon sananin talauci da kuma tsadar rayuwa.

Mutanen Venezuela na kokawa kan matsalar tattalin arziki da ke tilasta musu yin kaura zuwa kasashen ketare don samun ingantacciyar rayuwa
Mutanen Venezuela na kokawa kan matsalar tattalin arziki da ke tilasta musu yin kaura zuwa kasashen ketare don samun ingantacciyar rayuwa REUTERS/Douglas Juarez
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, mutane fiye da miliyan daya da rabi suka ficewa daga kasar tun daga shekarar 2015 bayan da matsalar tattalin arziki ta nakasa su.

Amma wata kididdiga ta daban na cewa akalla ‘yan kasar kusan miliyan biyu da rabi ne yanzu haka ke zaune a kasashen ketare, yayin da wata jami'ar Venezuela mai rassa a kasashen ketare ita ta fitar da nata alkaluman da ke cewa, adadin ya kai kusan miliyan hudu tun daga shekarar 1998, wato lokacin da shugaba Hugo Chavez ya karbin ragamar mulkin kasar.

Tomas Paez, masanin harkokin zamantakewa a Venezuela ya ce, tsakanin kashi 10 zuwa 12 cikin 100 na ‘yan kasar da ke kasashen waje, na zaune ne a kasashe fiye da 90 a fadin duniya.

Paez ya ce, akasarinsu na rayuwa ne a kasashen Colombia da Amurka da Spaniya, sai dai kaso mafi girma daga cikinsu na zaune a Peru.

Da dama daga cikin mutanen sun yi  hijira na a sawu, in da a  yanzu suke rayuwa a wasu sansanonin wucen- gadi da kuma kwana a kan tituna ba tare da wadataccen abinci ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.