Isa ga babban shafi
Amurka-Duniya

Amurka ta hana a sabunta wa’adin alkalin Kotun Kungiyar kasuwanci

Kasar Amurka ta hana a sabunta wa’adin aikin Shree Baboo Chekitan Servansing, alkalin Kotun Kungiyar kasuwanci ta duniya. Lamarin da ya kara jefa Kotun warware matsalolin da suka shafi kasuwanci cikin rudani a daidai lokacin da manufofin Shugaba Donald Trump na tsaurara haraji ga abokan cinikayya ya janyo matsaloli ga harkokin kasuwanci.

Donald Trump Shugaban Amurka
Donald Trump Shugaban Amurka REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A dai dai lokacin da Amurka ta tsaya kan manufar hana sabinta wa'adin,wasu daga cikin shugabanin kasashen Turai sun soma nuna fatar su na kawar da ido dangane da dogaro ga Amurka. Emmanuel Macron Shugaban Faransa a ganawa da dimbin jakadun Faransa Macron ya ce, kasashen Turai ba za su ci gaba da dogaro ga Amurka ba kan sha’anin tsaro, kuma ya rage gare su da su tabbatar da tsaro a yankinsu.

Kalaman Macron na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya nuna alamomin nesanta kansa daga tsarin kawancen kasashen da ke cikin kungiyar tsaro ta NATO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.