Isa ga babban shafi
Najeriya-Birtaniya

Najeriya da Birtaniya za su inganta harkar kasuwanci

Firaministan Birtaniya Theresa May ta sha alwashin inganta zuba jari da kuma dabbaka hada-hadar kasuwanci da Najeriya da zaran kasar ta fice daga cikin Kungiyar Kasashen Turai.

Firaministar Birtaniya Theresa May tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Abuja
Firaministar Birtaniya Theresa May tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Abuja https://politicsngr.com
Talla

Uwargida May wadda ta samu rakiyar ministocinta da masu zuba jari da kuma tarin 'yan kasuwa, ta bayyana haka ne lokacin da ta gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Abuja.

Jim kadan da kammala ganawar, Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffrey Enyeama ya shaida wa manema labarai cewa, shugabannin biyu sun sanya hannu kan yarjeniyoyi biyu da suka hada da tsaro da bunkasa tattalin arziki.

Yarjejeniyar tsaron ta kunshi taimaka wa Najeriya wajen tunkarar kalukubalen da take fama da shi ta fuskar atisayen soji da ayyukan ‘yan sanda da kuma kare hakkin bil’adama.

Gabanin isowarta Najeriya a ranar Laraba, Uwargida May ta fara ziyartar Afrika ta Kudu, yayin da kuma za ta nufi Kenya daga Najeriya.

Wannan ziyarar na cikin shirye-shiryen gwamnatin Birtaniya na dabbaka alaka tsakaninta da kasashen duniya bayan ficewarta daga Kungiyar Tarayyar Turai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.