rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Hukumar kasuwanci ta duniya Noma

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sauyin yanayi zai haifar da fari a duniya - Bincike

media
Binciken ya nuna cewa sauyin yanayin zai tilastawa kwari cinye abincin da al'umma ke nomawa matakin da zai haifar da gagarumin fari a sassan duniya matukar ba a dauki matakin magancewa ba. AFP/ PIUS UTOMI EKPEI

Masana sun bankado wani sabon bayanai da ke nuna cewar, sauyin yanayin da ake samu a duniya sakamakon dumamar yanayi, zai haifar da yunwa ga kwari da kuma tilasta musu cin kayan abincin da Bil Adama ke nomawa irin su alkama da masara da shinkafa.


Jagaoran binciken Scott Merrill daga Jami’ar Vermont, ya ce cin wadannan kayan abinci da suke kashi 42 na abincin da jama’a ke ci a fadin duniya, za su haifar da karancin abinci a duniya da kuma samun rikice rikice.

Binciken ya nuna cewar, dummar yanayin zai haifar da zafin da wadannan kwari zasu gamu da yunwa sosai, abinda zai tilasta musu cin abincin Bil Adama.

Masanan su ne za’a samu yaduwar kwarin a kasashe irin su Faransa da Amurka saboda yanayin da suke da shi.