rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamus Senegal Najeriya Ghana Bakin-haure Tarayyar Turai Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugabar Gwamnatin Jamus na ziyara a Afrika

media
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da wasu shugabannin Afrika REUTERS/Luc Gnago

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fara ziyarar wasu kasashen Afrika a yunkurin kasar na magance kwararar baki zuwa Turai da bunkasa harkokin kasuwanci da kuma yaki da 'yan ta’adda.


Merkel wadda ta isa Senegal a ranar Laraba ta samu kyakkyawar tarba daga shugaba Macky Sall

Gabanin fara ziyarar Uwargida Merkel, gwamnatin Jamus ta ce, akwai bukatar hana ‘yan Afrika daukar kasadar tsallaka teku da zummar shiga Turai don samun ingantacciyar rayuwa.

Bayanai sun ce, Merkel da ta samu rakiyar tarin shugabannin 'yan Kasuwa da masu zuba jari, za ta ziyarci Cibiyar Bunkasa Harkokin Kasuwanci ta Ghana kafin daga bisani ta gana da manyan 'yan kasuwa.

A Najeriya, bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari, Merkel za ta gana da shugaban Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma, Jean-Claude Kassi Brou.

Ziyararta na zuwa bayan ta Firaministan Birtaniya Theresa May, yayin da Jamus ta shiga cikin jerin manyan kasashen da ke inganta hulda da kasashen Afrika musamman ganin makomar tattalin arzikin yankin.