Isa ga babban shafi
Amurka

Shugaba Trump na zargin China da Turai da yiwa kasar sa illa

Shugaban Amurka Donald Trump yayi barazanar janye kasar daga cikin kungiyar kasuwanci ta duniya da ake kira WTO muddin kungiyar taki sauya yadda take mu’amala da ita.

Huldar kasuwanci tsakanin Amurka da manyan kasashen Duniya
Huldar kasuwanci tsakanin Amurka da manyan kasashen Duniya REUTERS
Talla

Trump yace kungiyar da aka kafa domin gindaya sharudodin kasuwancin Duniya da kuma sasanta rikicin kasashe na kaucewa dokokin da aka shinfida mata.

Shugaban na Amurka na zargin China da kasashen Turai da yiwa kasar sa illa wajen harkokin kasuwancin.

Kalaman Shugaban Amurka na zuwa dai-dai lokacin da ake shirin soma babban taron tattalin arziki da zai hada Shugabanin Africa da na China a Beijing.

Taron na wannan shekara zai mayar da hankali zuwa manyan batutuwa da suka shafi huldar kasuwanci tsakanin China da Africa, wacce da dama daga cikin masana tattalin arzikin yankin suka bayyana goyan bayan su a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.