Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinawa

Isra'ila ta yi maraba da janye tallafin Amurka ga Falasdinawa

Isra’ila ta yi maraba da matakin Amurka na Janye tallafin da ta ke sanyawa a asusun agazawa ‘yan gudun hijirar Falasdinawa na Majalisar Dinkin Duniya.

Karkashin shirin baya ga Falasdinawa milyan 5 da ke cin gajiyar tallafin akwai kuma yaran Falasdinawa kusan dubu dari biyar da 26 da hukumar ta UNRWA ke daukar nauyin karantun a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Lebanon da Syria da kuma Jordan.
Karkashin shirin baya ga Falasdinawa milyan 5 da ke cin gajiyar tallafin akwai kuma yaran Falasdinawa kusan dubu dari biyar da 26 da hukumar ta UNRWA ke daukar nauyin karantun a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Lebanon da Syria da kuma Jordan. REUTERS/Muhammad Hamed
Talla

Shirin Tallafawa Falasdinawan karkashin hukumar UNRWA wanda Amurka ke bayar da kaso mafi tsoka wajen tafiyar da shin a agazawa akalla Falasdinawa miliyan 5 da rikici ya raba da muhallansu.

Amurkan da Isra’ila na zargin cewa asusun wanda aka asassa kusan shekaru 70 na bayar da dama ga tarin Falasdinawan da ke damar komawa muhallansu bayan yakin 1948 da ya kai ga kafa kasar Isra’ila ci gaba da zama a sansanin ‘yan gudun hijira saboda agajin da su ke samu.

A jiya Juma’a ne Amurkan ta tabbatar da janye duk wani tallafi da ta ke bai wa asusun wanda dama tun a bara ta fara barazanar janye jiki.

Wata majiya daga fadar gwamnatin Isra’ila ta ce Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi maraba da matakain na Amurka wanda ya jima yana fatan kasancewarsa.
A cewar Isra’ila tallafawa Falasdinawan da tarin duniya daga Majalisar Dinkin Duniya shi ne ke rura wutar rikicin da su ke ci gaba da assasawa a yankin gabas ta tsakiya.

Jakadan Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya Hossam Zomlot ya ce Amurkan ta bijirewa nauyin da ya rataya akanta wanda aka cimma matsaya tsakaninta da Majalisar tun a shekarar 1949.

Karkashin shirin baya ga Falasdinawa milyan 5 da ke cin gajiyar tallafin akwai kuma yaran Falasdinawa kusan dubu dari biyar da 26 da hukumar ta UNRWA ke daukar nauyin karantun a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Lebanon da Syria da kuma Jordan.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ko kadan hukumar ta UNRWA ba zata girgiza da ficewar Amurka ba, maimakon haka zata mika kokon bararta ga wasu kasashe don ci gaba da aikin tallafin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.