Isa ga babban shafi
Brazil

Kotu a Brazil ta soke takarar Lula Da Silva

Jam’iyyar tsohon shugaban Brazil Lula Da Silva ta bayyana furucin ta yan lokuta bayan da alkalan kotu zabe suka yi watsi da bukatar tsohon Shugaban kasar na tsayawa takara.Alkalan a zaman su na yau asabar sun bayyana takarar tsohon Shugaban kasar a zaben ranar 7 ga watan Oktoba a matsayin abinda ya kaucewa doka.

Lula Da Silva Tsohon Shugaban kasar Brazil
Lula Da Silva Tsohon Shugaban kasar Brazil REUTERS/Rodolfo Buhrer
Talla

A watan Afrilu shekarar 2018 bayan share kwanaki uku a cibiyar kungiyar kwadagon ma’aikatan karafe na Sao Bernado, tsohon Shugaban kasar Brazil Lula Da Silva ya mika kan sa zuwa jami’an tsaron Curtiba dake kudancin kasar inda suka tisa keyar sa zuwa gidan kaso da zai share shekaru 12 a tsare bisa laifi rashawa da cin hanci.

A shekarar da ta shude ne wata kotu a kasar ta Brazil ta yanke masa hukuncin dauri bisa laifin karbar rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.