Isa ga babban shafi
Falasdinu-Isra'ila

Amurka ta nemi hade Falasdinu da Jordan zuwa kasa guda

Shugaban Falasdinu Mahmud Abbas ya ce jami’an kasar Amurka da ke kokarin shiga tsakani domin warware rikicin Gabas ta Tsakiya, sun tuntube shi kan shirin su na hada Falasdinu da Jordan domin zama kasa guda.

Shugaba Mahmud Abbas ya shaidawa jami’an na Amurka cewar ya na maraba da tayin muddin Israila za ta kasance cikin sabuwar kasar da ake shirin kafawa tare da Jordan.
Shugaba Mahmud Abbas ya shaidawa jami’an na Amurka cewar ya na maraba da tayin muddin Israila za ta kasance cikin sabuwar kasar da ake shirin kafawa tare da Jordan. REUTERS/Mohamad Torokman
Talla

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya bayyana tayin da tawagar fadar shugaban Amurka a karkahsin Jared Kushner da Jason Greenblatt ta yi masa ne lokacin da yake ganawa da wakilan wata kungiyar zaman lafiyar Yahudawa a Ramallah, kamar yadda Hagit Ofran na kungiyar Peace Now ya sanar.

Ofran ya ce, shugaba Mahmud Abbas ya shaidawa jami’an na Amurka cewar ya na maraba da tayin muddin Israila za ta kasance cikin sabuwar kasar da ake shirin kafawa tare da Jordan.

Babu tabbacin lokacin da aka yi wa Falasdinawan tayi, ganin yadda shugaba Abbas yaki ganawa da wakilan Amurka tun bayan lokacin da shugaba Donald Trump ya amince da Birnin Kudus a matsayin Cibiyar Israila.

Fadar shugaban Falasdinawan ta tabbatar da ganawar da akayi da kungiyar fararen hular amma ba tare da bayani kan tayin hade kasar ba, yayin da kafofin yada labaran Israila suka wallafa rahoto kan tayin.

Wasu Yahudawa na goyan bayan shirin hade Falasdinu da Jordan domin kaucewa raba kasar da suke da ita yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.