Isa ga babban shafi
Brazil

Gobara ta cinye gidan tarihi mai shekaru 200 a Brazil

Wata mummunar gobara ta cinye gidan ajiyen kayayyakin tarihi na Brazil da aka kafa shekaru 200 da suka gabata a birnin Rio de Janeiro.

Ginin gidan tarihin Brazil ta gobara ta cinye a Brazil
Ginin gidan tarihin Brazil ta gobara ta cinye a Brazil REUTERS/Ricardo Moraes
Talla

Jami’an kashe gobara na ci gaba da kokarin kawar da wutar a gidan tarihin mai dauke da nau'ukan kayayyaki daban-daban sama da miliyan 20.

Shugaban kasar, Michel Temer a wani sakon Twitter ya bayyana bakin cikinsa da aukuwar ibtila’in wanda ya salwantar da ayyukan bincike da ilimi na tsawon shekaru 200.

Kawo yanzu babu rahoto game da wadanda suka samu rauni sakamakon gobarar  wadda ta tashi a yammacin Lahadi.

Kafafen talabijin na kasar sun nuna yadda gobarar ta mamaye daukacin ginin.

A farkon shekarar nan ne gidan tarihin ya yi bikin cika shekaru 200 da kafuwa.

An kafa gidan ne a zamanin Sarki Jao na biyar a shekarar 1818 kuma al'ummar kasar na kallon gidan tarihin a matsayin babban jigo ta fuskar  raya al'adu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.