Isa ga babban shafi
Faransa-Liberia

Faransa ta tuhumi tsohon kwamandan 'yan tawayen Liberia

Faransa ta tuhumi tsohon kwamandan ‘yan tawayen Liberia kan zargin aikata laifukan yaki da suka hada da azabtarwa da cin naman mutane a lokacin yakin basasar kasar a tsakanin shekarar 1993-1997.

Ana zargin Kunti K, da shigar da kananan yara cikin aikin soja
Ana zargin Kunti K, da shigar da kananan yara cikin aikin soja AFP PHOTO/Charles LOMODONG
Talla

Majiyar Sharia ta ce ana zargin tsohon Kwamandan da aka bayyana shi a matsayin Kunti K., da taka rawa a karkashin kungiyar 'yan tawayen ULIMO da aka kafa a wancan lokaci.

Har ila yau ana zargin Kunti K. da kisan kai da bautar da jama'a baya ga shigar da kananan yara cikin aikin soja.

An kafa kungiyar ULIMO ne da zummar yakar wata rundunar mayaka da ke karkashin jagorancin tsohon dan tawayen da ya zama shugaban kasa, Charles Taylor da yanzu haka ke zaman shekaru 50 a gidan kaso sakamakon taimaka wa mayaka a makwabciyar kasar wato Saliyo.

Kasar Liberia wadda ‘yantattun bayi daga Amurka suka kafa, ta gamu da yakin basasa har sau biyu, lamarin da ya lakume rayuka kimanin dubu 250 tsakanin shekarar 1989 zuwa 2003.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.