rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Amurka Amurka Donald Trump Barack Obama

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Obama ya bukaci Amurkawa su juya wa Trump baya

media
Barack Obama, tsohon shugaban Amurka na jawabi a jami'ar Illinois, ranar 7 ga watan satumbar 2018. REUTERS/John Gress

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya yi dirar mikiya a kan shugaban kasar mai-ci Donald Trump, inda ya bukaci magoya bayan jam’iyyar Democrat da kuma Republican su nuna rashin amincewa da kamun lodayin shugaban.


Tsohon shugaba Obama, a yau asabar zai gudanar da wani gangamin siyasa a jihar California a daidai lokacin da Amurkawa ke shirye-shirye kada kuri’ar tsakiyar wa’adin shugabanci da za a yi cikin watan nuwamba mai zuwa.

Trump dai na shan suka a fannoni da dama, inda hatta a cikin fadarsa wasu bayyana shi a matsayin wanda ba ya  da dadin mu’ammala, sannan kuma ba ya mutunta na tare da shi.